YA KAMA HANYAR TAFIYA LAGOS DOMIN TAYA TINUBU MURNA TARE DA BASHI KYAUTAR KEKEN DA YA JE MAKKA A KANTA
Kamar yadda yayi alƙawarin bayar da kyautar keken shi da ya je aikin Hajji akan ta, Alhaji Aliyu Abdullahi Obodo mazaunin Jos ya kama hanyar tafiya Lagos domin taya zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya Alhaji Bola Ahmad Tinibu murna tare da bashi kyautar keken da keken kamar yadda yayi alkawari.
Idan ba a manta ba, a watannin baya jaridar Zinariya ya wallafa labarin daga tashin shi daga Najeriya har isar shi Saudiyya.
Ita dai wannan keken Larabawa sun so Alhaji Aliyu Abdullahi Obodo ya Siyar musu a farashi mai tsada domin su ajiye ta a gidan tarihi amma ya ƙi yarda ya ce shi lallai zai dawo da ita gida ya ba duk wanda ya lashe kujerar shugaban kasar Najeriya.
Jaridar Zinariya zata cigaba da bibiyar wannan lamarin kuma zata kawo muku yadda lamarin zai kaya.
Comments
Post a Comment