Bambanci Tsakanin Alqur'ani Da Alhadith Alqudhsi.
Bambanci Tsakanin Alqur'ani Da Alhadith Alqudhsi.
1. Alqur'ani da hadisi Qudhsi dukkansu daga Allah suke, sai dai akwai bambance-bambance da rabe-rabe tsakaninsu.
2. A wajen Malaman shari'a Alqur'ani zancen Allah ne wanda ya saukarwa Annabinsa S.A.W. Alqur'ani littafi ne mai cike da mu'ujiza kuma ana karanta shi a sallah kuma lafuzansa daga Allah suke kai tsaye.
3. Alhadisul qudhsi ana rawaito shi ne daga Annabi S.A.W ma'anar hadisin tana komawa zuwa ga Allah ne amma Annabi ke furta lafuzansa, ba a karanta shi a sallah ko samun lada.
4. Alqur'ani ya bambanta da Alhadisul Qudhsi ta bangaren mu'ujiza da tahaddi.
5. Alqur'ani Mala'ika Jibrilu ne ya saukarwa da Annabi S.A.W shi.
6. Amma Alhadisul Qudhsi bai kasance kamar haka ba, wani lokacin Mala'ika Jibrilu kan kawo wa manzon Allah shi, a yayin da wani lokacin kuma Annabi S.A.W kan sami hadisin ta ilhama da dai sauran hanyoyi.
7. Alqur'ani babu kokonto a kan ingancinsa kuma ya kasu zuwa surori.
8. A yayin da Alhadisul Qudhsi bai kasance kamar haka ba, domin akan sami ingantacce, ana kuma samun mai rauni har ma maudhu'i akan samu daga gare shi.
9. Duk wanda ya karyata Alqur'ani ya kafurta, wanda ya karyata Alhadisul Qudhsi saboda raunin marawaicinsa bai kafurta ba.
Indabawa Aliyu Imam
Comments
Post a Comment