Rawa a TikTok na Ƙoƙarin Raba Adam Zango da Matarsa

Rawa a TikTok ne sanadiyyar saɓanin da muka samu da mata ta Safiyya. 

Daga Auwal Saleh Jos


Shahararren jarumin Kannywood Adam A Zango ya bayyana haka ne a wani video da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.


Jarumin ya ce babban abinda ya sa suka samu saɓani da matar shi da yanzu haka tayi yaji na tsawon watanni ita ce wayar salula. Inda ya ce wannan ƙaddara ce wacce bai isa ya guje mata ba domin shi baya son rabuwa da matarsa in ba ya zama dole ba.



Har wa yau, Adam Zango ya ce matar shi tana Siyar da kaya kafafen sada zumunta sannan kuma tana yin adashe wanda ita ce uwar adashen amma bata faɗa mishi hakan ba sai daga baya ya gane hakan.


Adam Zango ya ce matarsa ta karya dukkan alƙawarin da suka yi na zamantakewa. Babban dalilin da ya sa ya ce ta tafi gidansu shine taje gidan lallai tayi lallen ta saka a TikTok tana rawa. "Wannan dalilin ne ya sa nace ta tafi gidan su domin ta karya min ƙa'idojin da na gindaya mata" in ji Adam Zango.


Daga ƙarshe Adam Zango ya ce ya gindaya wa matarsa wasu sharuɗa inda yace in dai ta amince da dawowa gidansa to dole sai ta daina amfani da wayar da ba a saka mata data sai dai kawai ayi kira. Sannan kuma sai ta daina yin kasuwanci a social media Kuma Adam Zango yayi alƙawarin zai canja mata gida domin su cigaba da zama idan ta amince da sharuddan da ya gindaya mata. Wanda kuma iyayen matarsan suke ƙeƙashe ido suka ce basu yarda ba domin hakan zai takurawa ƴarsu.


Adam Zango ya ce daga yanzu zuwa kowane lokaci komai zai iya faruwa tsakanin shi da matar shi; ko kome ko saki.

Zango yace masoyansa suyi haƙuri da duk abinda ya biyo baya.
 






Comments