GARIN DAƊI NA NESA: Qatar ta zaftare kuɗin kayan masarufi saboda Watan Azumi
GARIN DAƊI NA NESA: Qatar ta zaftare kuɗin kayan masarufi saboda Watan Azumi
Daga Auwal Saleh,Jos
Hukumomar kula da farashin kayayyaki a ƙasar Qatar da sanar da zaftare farashin kayan masarufi lura da karatowar watan Azumin Ramadan wanda zai fara aiki daga ranar Laraba har zuwa ƙarshen watan Ramadan.
An rage ƙuɗaɗen kayan masarufi sama da 100 domin samar da sauƙi ga ƴan ƙasa da kuma basu damar bautar Ubangiji cikin nutsuwa kamar yadda hukumar kula da kaya ta Qatar ta sanar.
Daga cikin kayan da aka rage farashin su sune: zuma, shinkafa, fulawa, madara, masara, ruwan gora, lemun gora, dabino, takarda, pampers, ƙwai, taliya, sabulu, kaji, nama, kifi, gishiri, kayan miya, man gyada da sauran kayan aikin gida na yau da kullum.
Comments
Post a Comment