Qatar 2022: Tsakanin Addini, Al'ada da Tattalin Arziƙi
Qatar 2022: Tsakanin addini, al'ada da arziƙi
Cikin yardar Allah, an kammala gasar cin kofin duniya cikin lumana kuma ƙasar Argentina ta lashe gasar karo na uku a tarihi.
Ba shakka, wannan gasar ta zo da sauyi akan yadda aka saba gabatar da gasar. Babban sauyi uku sune: Addini, Al'ada da kuma ƙarfin tattalin arziki.
ADDINI: Lallai ƙasar Qatar ta nunawa duniya cewa tana da addini; addinin kuwa shine Musulunci. Hasali ma shine babban dalilin arziƙin su kamar yadda Sarkin su ya bayyana.
Ƙasar Qatar tayi amfani da irin salon karantarwa da Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya koyawa Musulmai; wato kira ga addini cikin hikima tare da kyautatawa. Hakan ya fito fili domin ƙasar Qatar ta hana siyar da giya a filayen wasa bakwai da aka fafata. Hasali ma, shehun malami mai fatawar ƙasar Sheikh Tamim bin Hamad II ne ya tsara yadda gasar zata kasance ta yadda za a kula da haƙƙin Allah.
Bayan haka, an samar da masallatan wucin gadi domin masallata suyi sallah tare da nunawa waɗanda ba musulmi ba yadda ake Sallah a aikace. An liƙa zikirori da Hadisan Annabi Tsira da Amincin Allah ya tabbata gare shi wadanda suke koyar da kyawawan ɗabi'u.
A al'ada ta irin wannan gasar, kafin a kammala ta, akan samu ƙorafe-ƙorafe akan fyaɗe ga mata da kuma yaɗuwar alfasha kamar luwaɗi da tsafe-tsafe da sauran su. Wannan karon abin ba haka ya kasance ba. Qatar ta zana jan layi ga masu wannan munanan ɗabi'un. Kuma ALHAMDULILLAH, kwalliya ta biya kuɗin sabulu domin kuwa an samu mutane da yawa da suka musulunta.
AL'ADA: Lallai Qatar sun nunawa duniya cewa su mutane ne masu riƙo da al'adun su, wato basu yi fatali da kyawawan al'adu da suka gada daga iyaye da kakanni ba. Sun nuna irin al'adar su wa duniya kuma duniya ta gani. Duk wani abu da ya saɓawa al'adar su sun ja layi akan shi. Wannan ya fito fili kamar yadda muka ga yadda Larabawa suke irin shigar al'adar su tare da iyalan su. Hasali ma, bayan an miƙa kambun zakaran wasa ga Leo Messi, sai aka lanƙaya masa alkyabba domin nuna muhimmancin al'adar Larabawa wa duniya.
TATTALIN ARZIƘI: Kai ba sai an faɗa maka ba, daga ganin taswirorin filayen da aka buga wasan gasar nan ka san cewa an kashe kuɗi.
Hukumar dake kula da gasar tace an kashe dala biliyan ɗari biyu da ashirin domin gabatar da gasar. Ka san nawa kenan a Naira?
Tiriliyan 98.1 kenan. Kasafin kuɗin Najeriya na shekara biyar kenan.
Kai ba sai an faɗa maka ba ka san cewa ƙasar Qatar tana da ƙarfin tattalin arziƙi wanda kaso saba'in yana zuwa ne daga man fetur.
Ƙididdiga ta nuna cewa ƙarancin albashi a shekara na ɗan ƙasar Qatar ya kai dala dubu ɗari da ashirin. Wato kimanin miliyan tamanin da shida a Naira (a farashin bayan fage).
Daga ƙarshe dai, an buga wasa, waɗanda Allah ya ƙaddara sun lashe gasa. Masu kafa tarihi sun kafa. Kuma Qatar ta isar da saƙon ta ga duniya kuma duniya ta ga saƙon.
Suna na Auwal Saleh. Ni ɗan
jarida ne, mazaunin Jos.
Comments
Post a Comment