Bayan dukan Sulen Garo da kofi, Alhassan Ado Doguwa ya fasawa Ahmad Aruwa baki
An kuma: Bayan dukan Sulen Garo da kofi, Alhassan Ado Doguwa ya fasawa Ahmad Aruwa baki
A jiya ne wani sabon faɗa ya sake kaurewa tsakanin jiga-jigan jam'iyyar APC na jahar a yayin da har ta kai da ba hammata iska tsakanin Ahmad Aruwa da Alhassan Ado Doguwa.
Lamarin dai ya faru ne jiya a yayin da Aruwa ya halarci taron karrama mahaifiyar Alhassan Ado wand shi Alhassan ɗin ya shirya domin karrama mahaifiyarsa saboda irin gudunmawar da ta bashi a rayuwarsa.
Wakilin Daily Nigerian ya rawaito cewa lokacin da ake ɗaukan hoto ne dai Alhassan ya doki Aruwa a baki har sanda bakin ya fashe. Sai Alhassan Ado ya ƙara da cewa "Kai maciyin amana ne. Ka ci amana ta don haka ka fita min daga gida na"
Rahotanni sun nuna cewa Ahmad Aruwa haka ya fita daga gidan Alhassan Ado Doguwa jina jina yana sharɓan kuka tare da nadamar halartar taron.
Daily Nigerian tayi ƙoƙarin jin ta bakin Alhassan Ado Doguwa amma hakan ya ci tura.
Idan mai karatu bai manta ba, a makon nan irin wannan faɗan ya kaure tsakanin Alhassan Ado da Sulen Garo har ta Alhassan ya bugawa Sulen Garo kofin shan
shayi a kai
Comments
Post a Comment