KOTU TA BAYAR DA UMARNIN KAMA SHUGABAN HUKUMAR EFCC
KOTU TA BAYAR DA UMARNIN KAMA SHUGABAN HUKUMAR EFCC
Kotun FCT High Court Abuja ta bada umarni wa Shugaban 'yan Sandan Nigeria IGP Usman Baba Alkali ya gaggauta kama shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) Abdulrashid Bawa
Alkaliyar da ta jagoranci zaman Kotun Justice Chizoba Oji tace Abdulrashid Bawa yayi biris da umarnin Kotu na ranar 21-11-2018 inda Kotu ta umarni hukumar EFCC ta dawo da wata Mota kirar Range Rover da kuma kudi kimanin Naira Miliyan 40 ma wanda ya shigar da kara amma hukumar taki
Don haka Abdulrashid Bawa da yake shugabantar hukumar a yanzu shima ya bijire wa umarni Kotu tare da raina kotu, don haka Alkaliyar tace a kamashi sannan a turashi gidan yarin Kuje dake Abuja
Comments
Post a Comment