Barrister Salis: Matashin Lauyan da Ya Kare Martabar Annabi SAW
Barrister Umar Saleeth Umar |
Barrister Saleeth Omar kenan.
Lauya mai zaman kansa, kuma mai kamfanin S.S Umar & Co.
Rubutawar Ibrahiym A. El-Caleel
A shekarar 2020 wani mulhidi a Facebook yayi ɓatanci ga janabin Manzon Allah ﷺ kamar yadda ya saba. Barriser Saleeth a matsayin shi na masoyin Manzon Allah ﷺ yace lokaci yayi da za'a bambancewa wannan mulhidi tsakanin ƴancin faɗin ra'ayi (Freedom of Speech) da kuma ƙetare haddi (Crossing of boundaries).
Don haka yayi amfani da kamfaninsa mai albarka ya kai ƙorafi (complaint) ga kwamishinan ƴan sanda. Shima kwamishinan da yake ɗan albarka ne, bai yi wasa da harkar ba. Aka kama mulhidin aka tsare, aka tanadi hujjoji da komai da za'a gabatar a gaban kuliya. Ƙarshe dai a watan Aprilun wannan shekarar kotu ta kama mulhidi da lefinsa, kuma ta yanke masa hukuncin ɗauri na shekaru 24!
Me ya biyo baya?
BBC a irin yadda suke da himma wajen shiga ƙasashen Afirka don zaƙulo irin waɗannan abubuwa, su yaɗa a duniya cewa Afirka ba'a waye ba, ana takurawa mutane akan zaɓin hanyar rayuwarsu, sai suka yi wani shiri ranar Litinin. Sunan shirin wai "The cost of being an atheist". Ma'ana wai "Farashin da ake biya in an zama mulhidi".
Ka duba makirci irin na BBC. Shi fa wannan mulhidi ba saboda ilhadi aka kaishi ƙara ba, kuma ba saboda ilhadi aka ɗaure shi shekaru 24 ba. Ba ko ɗaya. Duk abinda ya same shi ya same shi ne saboda ya ƙetare haddi yayi ɓatanci ga Manzon Allah ﷺ wanda yake da miliyoyin masoya a Najeriya waɗanda wannan aiki na Mubarak zai iya kawo abinda ba'a tsammaninsa! Kuma a cikin wannan shirin sai da Barrister Saleeth ya sake nanatawa makirar interviewer ɗin cewa: a ƙarƙashin "penal code" aka kama Mubarak da lefi, saboda ayyukansa zasu iya tada fitinar da zata afkawa waɗanda basu ji ba basu gani ba. Ba ma batun Islamic Law bane. Da ace Islamic Law ake sosai a ƙasar, ai da yana cikin waɗanda suka riga mu gidan gaskiya da jimawa. Da ba zai ma samu damar zaman gidan yari na shekaru 24 ba. Saboda haka, dimukraɗiyyah ta daƙile asalin hukuncin ma da ya rataya a wuyansa tun farkon al'amari.
Abinda ya ja hankalina gameda Barrister Saleeth shine yadda ya faɗawa wannan interviewer cewa shi dai ya taya matar Mubarak da ɗansa takaicin abinda ya faru. Yace amma fa ba wai jimami yake wai don an ɗaure Mubarak tsawon shekaru 24 ba. A'a. Yana taya su takaici ne saboda ya jefa kanshi cikin wata fitinar da tasa iyalansa ba zasu kasance tare da mai kula da su ba tsawon waɗannan shekaru.
Abin sha'awa shine yadda wannan Barrister yake da tazahuri da addininsa, kuma yake iya kallon makirar ƙiri-ƙiri ya nuna mata cewa babu wasa a cikin sha'anin addininsa. Har aka kammala wannan shirin bai kuskure ba wajen nunawa interviewer ɗin irin yadda yake matuƙar ƙimanta addininsa. Wannan abin sha'awa ne, kuma abinda zamu iya koya ne daga wannan bawan Allah da muke kyautatawa zato.
Allah Ya saka mishi da alheri. Allah Ya sanya albarka a wannan kamfani nashi, ya ƙara masa clients masu gaskiya kuma masu nauyin aljihu. Allah Ya kuma ƙara mana irinsu a cikin al'ummah tare da yi musu jagora zuwa ga daidai, Amin.
Wannan cuta ta ilhadi da take yawo, Allah Ya kawo mana sauƙin ta. Allah Ya shiryi waɗanda suka faɗa mata. Allah Ya kare mu da zurriyar mu daga kafirci.
Amin.
Su kuwa BBC sun taimaka wajen yaɗawa al'ummah wannan labari da ke nuna cewa ashe dai za'a iya ɓullowa ta penal code wajen tabbatar da cewa an hukunta mutane irin su Mubarak da su Deborah da su Isioma Daniel. Wanda mu da son mu ne, da Islamic Law ɗin ya fi ƙarfi a yankunan musulman ƙasar. Amma dai duk da haka wannan ɗin zai iya taimakawa wajen rage wannan ɓarnar. Gaishe ka Barrister Saleeth!
Ga link ɗin videon BBC: https://youtu.be/uoHCqjR-Dts
Comments
Post a Comment