Barkwanci: Labarin Wani Mutum da Matarsa
Sunje yawon buɗe Ido zuwa wani Rafi da ake kiwon Kadoji (Crocodiles) .
Mai Rafin yace: Wanda ya shiga cikin wannan rafin zan ba shi Dala Miliyan 10. Kowa ya yi tsit.
Can sai aka ji wani ya yi tsalle ya faɗa. Ko da afkawarsa cikin rafin nan sai suka ga babu wani abu da ya same shi. Ashe duk Kadojin na roba ne. Take ya lashe kyautar kuɗi.
Bayan mutumin nan ya koma Hotel tare da matarsa, sai yace mata: Wallahi wani ne ya tura ni cikin rafin nan, ba da son raina na faɗa ba.
Matarsa ta kalle shi cikin murmushi tace: Ai ni na turaka...
Darasi: "Behind every successful Man, there is always a Woman to give him a little push" 😊😊😊
Rabiata Abdulmumin ce ta turo mana.
Comments
Post a Comment