Akwai Sharholiya Cikin Bukukuwan Mu

 AKWAI SHARHOLIYA A BUKUKUWAN MU

Mubarak Ibrahim Lawan 


Sharholiya kam akwaita gurin ƴan Najeriya. Ka kalli bukukuwanmu, gine-ginenmu da suturunmu. A nan ne za ka gane muna da Sharholiya. A bikin bazde kaɗai a na ɓatar da miliyoyin kuɗi. In kuwa a ka zo bikin aure, wayyo Allah! Bayan kuɗin da a ke ɓatarwa a Events, da na abinci, to har tsirfar kyauta ga masu halartar biki a ka ɓullo da ita! A bikin ƴaƴan Sarkin Noma har iPhone mafi tsada a ka rabawa mahalarta saboda ainihin sharholiya. 


Shiko talaka, sai iyayen amarya da ango sun ƙarar da tarinsu na shekaru da dama wajen kwaikwayon manyan can. Da yawa a na gama biki za ka ga kowa ya koma fankan-fayau. Angon sai ya ci bashin kayan abinci; uwar amarya sai ta ɗau lokaci bayan biki ba ta gama biyan bashi ba. Duka dai an ƙure kai kawai don kar a ci bashin sharholiyar biki!


Tabbas muna da Sharholiya musamman a yanda mu ke rigegeniya wajen tafiya shaƙatawa Dubai, Ingila ko Saudiya. Daga sama, Sarkin Noma Baba Manjo ya keta hazo sama da sau 50 a cikin shekarun nan bakwai. Ƴan ƙasa kuma sun tabbatar cewa duka tafiye-tafiyen ba nasu ba ne, sharholiyarsa ce kawai da ƙara'i, tunda ba su ga alfanunsu ba ko kaɗan cikin ƙasar. Hakana an ga hotunan kyawawan iyalinsa a cikin jirgi aka-aka a lokacin da su ke kan hanyar zuwa London ko Dubai. Haka dai abin ya taho har zuwa ƙasa.


Sharholiyar ƴan Najeriya fa ba ta tsaya a nan ba. Ka kalli yanda Baba Manjo ke ɓarje galla-gallan motoci a Villa. An ce yanzu haka ma za a fitar da miliyan dubu biyu don canja motocin ofishinsa. To ko motar "Night Rider" ko ta "James Bond" za a siyo ai sai haka. Ba komai! Sharholiyarce dai kawai! Don haka za ka ga ƴan ƙasa na gari na koyi. Kullum cikin canjin mota su ke. Motocin miliyoyi a ke hawa. Akwai mutane irin su Dino Melaye da su ka yi gonar motoci irin su Bugati saboda tsabagen riƙo da noma a kan ɗariƙar Baba Manjo!


Jama'a, a rage sharholiya, a alkinta kuɗi kuma a koma gona! In ma ba ku yarda da Allah ba, ai yunwar cikinku ta gaya muku tunda Sarkin Noma ya ruhe iyakokin ƙasa. Ku yi noma ko a kashe ku da yunwa! Ku yi noma kuma don ku samu damar yin ado! Ni kam na tai gona! Sai anjima!


Mubarak!



Comments